MALAM IBRAHIM SHEKARAU GOGA KA SAN HANYA

Daga: Bikisu Yusuf Ali Me Ya Sa Wasu Ke Ganin Gogaggen dan Siyasa ne ya Dace da Majalisar Dattawa? Nazari Ta Fuskar Malam Ibrahim Shekarau Majalisar Dattawa ita ce babbar…

Sulaiman Umar August 06, 2026  ·  12:00 AM
| 25 Views
MALAM IBRAHIM SHEKARAU GOGA KA SAN HANYA
MALAM IBRAHIM SHEKARAU GOGA KA SAN HANYA

Daga: Bikisu Yusuf Ali

Me Ya Sa Wasu Ke Ganin Gogaggen dan Siyasa ne ya Dace da Majalisar Dattawa? Nazari Ta Fuskar Malam Ibrahim Shekarau Majalisar Dattawa ita ce babbar majalisar dokoki ta Najeriya mai wakiltar mazabun sanatoci 109. Babbar aikinta ita ce kirƙirar dokoki, sa ido kan ayyukan gwamnati, wakiltar muradun al'umma da kuma tantance wasu muƙaman gwamnati kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya tanada. Saboda muhimmancin wannan majalisa, masu nazarin siyasa sukan yi la'akari da gogewa ta ilimi da tarihin shugabanci lokacin nazarin cancantar 'yan takara.Haka ana bukatar mai baki da kishi da iya magana cikin mutane da iya Turanci sannan mai hazaka da hikima kuma jajirtacce marar tsoro. Duk wanda zai zama wakili bayan majalisa a jiharsa da yankinsa sai ya zama mai sanin matsaloli kuma mai saukin kai da tallafar al’umma. Bai dace mai girman kai da rashin tausayi ko son kai da son zuciya ya zama wakilin majalisar dattawa ba. Ko da jin sunan wakilcin ya dace ne da mai shekaru da nutsuwa da gogewa wanda ya saba da hidimar mulki da jama’a wanda ya ga jiya ya ga yau. Ayyukan Majalisar Dattawa Majalisar Dattawa tana da manyan ayyuka kamar haka: Samar da dokoki domin zaman lafiya, tsari da kyakkyawan shugabanci. Wakiltar bukatu da muradun al'ummar mazabar da sanata yake wakilta. Sa ido kan yadda ma'aikatu da hukumomin gwamnati ke aiwatar da kasafin kuɗi da ayyukansu. Tattauna manyan matsalolin kasa kamar tsaro, ilimi, lafiya da tattalin arziki. Tantance wasu mukaman gwamnati da shugaban kasa ke nadawa, kamar ministoci da wasu manyan jami'ai, kamar yadda doka ta tanada. Me yasa Malam Ibrahim Shekarau ya cancanta da wannan kujera? Malam Ibrahim Shekarau gogaggen malamin makaranta ne da ya jima a harkar koyarwa da sha’anin jama’a, ya taba zama Gwamnan Jihar Kano na wa'adi biyu sannan ya rike mukamin Ministan Ilimi na Tarayya. Ya taba zama sanata. Malam Shekarau basarake ne. Saboda wannan gogewa, masu nazari suna kallon tarihin aikinsa domin fahimtar irin gudummawar da zai iya bayarwa idan ya rike wannan matsayi wanda ba bako ba ne a wurinsa ko wani sabon mukami. A bangaren dokoki, gogewar gudanar da gwamnati na iya taimaka wa dan majalisa wajen fahimtar yadda manufofi ke aiki a aikace da kuma yadda dokoki za su iya shafar rayuwar jama'a. A bangaren wakilci, wanda ya taba shugabanci kan iya amfani da kwarewarsa wajen tattaunawa da hukumomin gwamnati da kuma gabatar da bukatun al'mmarsa a zauren majalisa. A bangaren sa ido kan ayyukan gwamnati, gogewar aiki a matakin jiha da tarayya na iya taimaka wa ɗan majalisa wajen yin nazari kan manufofi, kasafin kuɗi da aiwatar da ayyukan gwamnati bisa abin da ya koya daga ƙwarewarsa. Masana siyasa suna ganin cewa cancantar dan takara ga Majalisar Dattawa ba ta ta'allaka ga suna ko shahara kadai ba, har ma da ikon yin doka da wakiltar jama'a, da kuma sa ido kan ayyukan gwamnati. Saboda haka, masu zaɓe kan yi nazarin tarihin kowane dan takara da gogewarsa kafin su yanke hukunci.

Advertisement

NRS Gateway

Written by

Sulaiman Umar

Sulaiman Umar is an editor and reporter with extensive experience in economic journalism, analyzing financial and agricultural developments in Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 4 + 2?