Jami’an Tsaro Sun Gayyaci Gwajo-Gwajo Kan Wata Hira a Facebook

Daga Wakilanmu @Katsina TimesMajiyoyi daban-daban sun tabbatar wa da Katsina Times cewa jami’an tsaro masu fararen kaya sun gayyaci Alhaji Yau Umar Gwajo-Gwajo, mai bai wa Gwamnan Jihar Katsina shawara…

Katsina City News August 27, 2026  ·  12:00 AM
| 98 Views
Jami’an Tsaro Sun Gayyaci Gwajo-Gwajo Kan Wata Hira a Facebook
Jami’an Tsaro Sun Gayyaci Gwajo-Gwajo Kan Wata Hira a Facebook

Daga Wakilanmu @Katsina Times

Majiyoyi daban-daban sun tabbatar wa da Katsina Times cewa jami’an tsaro masu fararen kaya sun gayyaci Alhaji Yau Umar Gwajo-Gwajo, mai bai wa Gwamnan Jihar Katsina shawara kan harkokin siyasa, domin yi masa tambayoyi kan wata hira da ya yi a wani shafin Facebook.


Majiyoyinmu sun bayyana cewa gayyatar ta biyo bayan wasu kalamai da Gwajo-Gwajo ya yi a yayin hirar, wadanda wasu ke ganin za su iya haifar da ƙarin saɓani da tunzura jama’a.


A cewar majiyoyin, Gwajo-Gwajo ya amsa gayyatar jami’an tsaron tare da bayyana matsayinsa a rubuce, inda ya yi bayanin abin da yake nufi da kalaman da ya yi yayin hirar.


Majiyoyin sun kuma ce an cimma wata yarjejeniya tsakanin jami’an tsaron da Gwajo-Gwajo dangane da batun hirar da ya yi a shafin Facebook.


A ‘yan kwanakin nan, siyasa a Jihar Katsina na ci gaba da ɗaukar zafi, musamman a tsakanin wasu ‘yan jam’iyyar APC. 

Advertisement

NRS Gateway


Wasu masu lura da al’amuran siyasa na ganin cewa akwai masu ƙara rura wutar rikicin siyasa domin cimma muradunsu na kashin kansu.


Katsina Times ta yi ƙoƙarin jin ta bakin Alhaji Yau Umar Gwajo-Gwajo da kuma wani jami’in tsaro da ya yi masa tambayoyi lokacin da ya kai ziyara wajen jami’an tsaron, amma ƙoƙarin bai yi nasara ba har zuwa lokacin kammala wannan rahoto.


Katsina times 

@ www.katsinatimes.com 

Facebook page: katsina city news 

Facebook page ,Jaridar Taskar labarai 

07043777779

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 6 + 8?