Monday Ashibogwu Ya Ba Mawallafa Kafofin Yanar Gizo Shawarwari Kan Yadda Za Su Samu Kudaden Shiga Daga Aikin Jarida Na Yanar Gizo

Daga Katsina TimesTaron Shekara-Shekara da ke gudana na Ƙungiyar Mawallafa Kafofin Sadarwa na Yanar Gizo (GOCOP) ya ci gaba da ƙarfafa mambobinsa ta hanyar gudanar da samun horo na musamman,…

Katsina City News October 10, 2026  ·  12:00 AM
| 52 Views
Monday Ashibogwu Ya Ba Mawallafa Kafofin Yanar Gizo Shawarwari Kan Yadda Za Su Samu Kudaden Shiga Daga Aikin Jarida Na Yanar Gizo
Monday Ashibogwu Ya Ba Mawallafa Kafofin Yanar Gizo Shawarwari Kan Yadda Za Su Samu Kudaden Shiga Daga Aikin Jarida Na Yanar Gizo



Daga Katsina Times


Taron Shekara-Shekara da ke gudana na Ƙungiyar Mawallafa Kafofin Sadarwa na Yanar Gizo (GOCOP) ya ci gaba da ƙarfafa mambobinsa ta hanyar gudanar da samun horo na musamman, inda aka gudanar da wani horo mai taken ‘Samun Ƙu]aɗen Shiga Daga Kasuwancin Kafofin Sadarwa na Yanar Gizo; Samun Ƙudin Shiga Wajen Tallace-tallace da Labarai Da Aka Ɗauki Nauyi’ a otal din Radisson Blu da ke Ikeja, Jihar Lagos, Najeriya.


Dr Monday Ashibogwu, Babban Darakta na Kamfanin Billsbox Services Limited kuma Mawallafin Quick News Africa, shi ne ya gabatar da wannan lakca.


Ya garga]i mawallafa cewa harkar tallace-tallace da aka gina kan yawan ziyartar shafuka (pageviews) tana raunana, yayin da masu karatu suka koma sauran kafofin sadarwa. Ya ]ora wannan sabon yanayi kan }aruwar amfani da manhajojin bincike da }ir}irarriyar Basira ta Artificial Intelligence (AI) wajen ba masu karatu amsoshi kafin ma su kai ga ziyartar shafin gidan jaridar.


Sabanin haka, ya jaddada cewa mawallafan yanar gizo na Najeriya suna da wata babbar kaddara da harkar tallace-tallace ke rainawa, wato tsantsar amincewa da ke tsakanin su da masu karatunsu, inda ya }ara da cewa babban aikin shi ne sauya wannan amincewa zuwa hanyar samun ku]a]en shiga.


Ya binciki hanyoyi guda shida na samun ku]a]en shiga ba ta hanyar tallace-tallace ba (zama mambobi, shirya taro, horarwa, adana bayanai da fashin baki, ba da lasisi, da kuma samar da kayayyaki da ayyuka) ta hanyar yin amfani da misalai daga duniya, Afirka, da Najeriya.


Shekaru biyu da suka gabata, ya nuna cewa GOCOP tana da kwa]ayin koyon hanyoyin samun ku]a]en shiga ga mawallafa, inda ya ce a yanzu an samu sauyi mai tayar da hankali.


Ya ce: “Da fari, masu karatu suna barin }ofofin mawallafa kamar yadda rahoton 'Digital News Report 2026' na Cibiyar Reuters ya tabbatar, wanda ya gudanar da bincike kan kusan mutane 100,000 a kasuwanni 48.


“Abu na gaba shi ne cewa yawan zirga-zirgar maziyarta shafuka da mawallafa suka dogara kanta yana raguwa. Ya ce binciken da aka yi kan shafukan labarai sama da 2,500 ya nuna cewa ziyarce-ziyarcen da ake samu daga manhajan bincike na Google sun ragu da kashi guda cikin uku a fa]in duniya tsakanin Nuwamba 2024 da Nuwamba 2025. Mawallafa suna tsammanin sake raguwa da kashi 43 cikin ]ari a cikin shekaru uku masu zuwa.”


Abu na uku, ya ce ku]i yana bin inda masu karatu suke ne, saboda haka tsarin tallace-tallace da aka gina kan yawan danna shafi ba zai ]ore ba idan wata kafar sadarwa ta daban ce take kar~e wannan ziyara, ko kuma idan ta}aitaccen bayani na }ir}irarriyar Basira ta AI ya amsa wa mai karatu kafin ma ya isa shafin mawallafin.


Ya nuna garga]in da Ƙungiyar Editocin Najeriya (NGE) ta yi game da yiwuwar dur}ushewar kafofin sadarwa. Ya c,e Najeriya tana jin ra]a]in wannan raguwa sosai.


Ya kuma bayyana waɗansu hanyoyin da ya ambata, ciki har da samun ku]a]en shiga daga masu karatu ta hanyar zama mambobi, inda ya ambaci wata jaridar ƙasashe waje da ke da mambobi masu karatu miliyan 1.4, wadda ta sami sama da fam miliyan 126 a shekarar da ta ƙare a watan Maris 2026.


Ya kuma ambaci ‘shirya taro da ikon tattara mutane’ a matsayin wata babbar hanyar samun ku]a]en shiga da mawallafa za su iya amfani da ita.


Dr Ashibogwu ya ce: “Kalandar rayuwa tana tare da mu. Yayin da zaɓen shekarar 2027 ke ƙarasowa, ana bu}atar shirya muhawara tsakanin ’yan takara, tattaunawa kan manufofi, da taron garuruwa a matakin jihohi. Mawallafin yanar gizo mai amintaka yana da kyakkyawan matsayi na gudanar da wa]annan abubuwa, da shara]i guda: kowane ]an takara za a ]ora masa sharu]]a iri ]aya da aka wallafa, ta yadda dandalin ba zai ta~a zama na sayarwa ga ~angare guda ba.”

Advertisement

NRS Gateway


Ya ambaci hanya ta hu]u a matsayin horarwa da ba da ayyuka, yayin da hanya ta biyar ta kasance adana bayanai, bincike, da fashin ba}i. Ya tunatar da mawallafan da suka da]e suna kawo rahotanni kan fagage daban-daban tsawon shekaru da dama cewa suna zaune ne a kan rumbun bayanai masu cike da albarka.


Game da ba da lasisi da kuma cinikin bayanai ya lurar da cewa wasu kamfanonin daban suna amfani da labaran mawallafan Najeriya domin samun ku]a]en kansu. “A watan Yulin wannan shekarar, biyo bayan takardar koke ta haɗin gwiwa da Ƙungiyar 'Yan Jarida ta Najeriya (NPO) ta shigar, wadda GOCOP ke cikin ta, Shugaban Ƙasa ya umarci Hukumar Kare Haƙƙin Masu Amfani da Kayan Aiki da Gasa (FCCPC) da ta gudanar da bincike kan yadda kamfanonin Meta, Alphabet, X da kamfanonin }ir}irarriyar Basira ta AI ke amfani da labaran Najeriya.


“Kada mu jira sakamakon binciken kafin mu shirya. Muna buƙatar ingantattun bayanai kan adadin masu ziyartar shafukanmu, adana bayananmu na baya, da halin da muke ciki na ku]a]en gudanarwa, da kuma kyakkyawan tsarin raba duk abin da aka samu tsakanin mambobi 127, manya da ƙana-ƙana.” Ya kuma ambaci samar da kayayyaki, ayyuka, da harkokin kasuwanci.


Ya ba da wasu mafita amma ya tambayi ta yaya mawallafi mai ma'aikata da kuma matsattsun ku]a]en albashi zai iya farawa. Farko, ya buƙaci mawallafa da su mallaki masu karatunsu na kansu. “Mabiyi a kafar sadarwa ta daban na aro ne. The Continent, wata jaridar mako-mako ta Nahiyar Afirka, ta gina masu karatunta ne ta hanyar tura jaridar kai tsaye ta manhajar WhatsApp,” in ji shi.


Dr Ashibogwu ya ƙara da cewa: “Ku faro saƙonnin 'newsletter' da kafar WhatsApp a wannan watan, kuma ku bi dokar kariya da adana bayanai ta Najeriya (Nigeria Data Protection Act) yayin da kuke tattara bayanan. Na gaba, ku zaɓi fanni na musamman. Labarai na gari tamkar kaya ne da ke ko’ina. Masu karatu da abokan kasuwanci suna biyan mawallafin da ya fi kowa sanin fanni guda, jiha guda, ko al'umma guda fiye da kowa.”


“Ku fara da hanya guda, ba guda shida ba. Ku zaɓi wadda ta fi kusa da abin da kuka riga kuka ƙware a kai, ku gudanar da ita na kwanaki 90, sannan ku auna sakamakon. Ku kare ɗakin rahotanninku. Kowace ɗaya daga cikin waɗannan hanyoyin tana samar da abokin kasuwanci wanda wata rana zai iya zama batun labari. Matakin amincinmu shi ne dukiyar da ke bayan dukkan waɗannan hanyoyi guda shida. Idan muka watsar da shi, ba mu da sauran abin da za mu sayar. Ku mi}a alhakin samun ku]a]en shiga ga mutum guda. Ku]in shiga da ya zama aikin kowa yakan koma ba aikin kowa ba,” in ji shi.


Masanin ya shaida wa mambobin cewa zamanin tallace-tallace ya koya wa mawallafa ƙidaya masu ziyartar shafukansu, amma; “Zamani na gaba zai saka wa wa]anda ke ƙidaya kyakkyawar dangantaka: mambobi, wakilai, 'yan horo, abokan kasuwanci da masu lasisi.”


Ya ci gaba da cewa: “Hasashen kasuwanci da Cibiyar Reuters ta ambata ya nuna cewa kasuwar kafofin sadarwa ta Najeriya za ta kai dalar Amurka miliyan 540 zuwa shekarar 2029, inda kusan rabinta za ta zama ta yanar gizo. Tambayar ita ce nawa ne daga cikin waɗannan ku]a]en zai isa ga mutanen da ke cikin wannan ]aki.”


Ya ba da shawarar cewa kowane mawallafi ya bar taron tare da sabuwar hanya guda ɗaya ta samun ku]a]en shiga da kuma gwajin kwanaki 90.


Ya kuma ba Ƙungiyar shawara da ta kafa kwamiti na dindindin kan ku]a]en shiga da lasisi, ta yadda lokacin da aikin hukumar sa ido ya ƙare, mambobi za su haɗu a teburin tattaunawa a shirye suke. “Muna da amincewar masu karatu. Bari yanzu mu gina kasuwancin da ya dace da wannan amincewar,” in ji shi.


A sa’ilin nan ne, Malachy Agbo, shugaban farko wanda ya assasa GOCOP, wanda yanzu shi ne Kwamishinan Ya]a Labarai na Jihar Enugu, wanda ya halarci taron, ya yaba da ci gaban da ƙungiyar ta samu zuwa yanzu.


Ya bayyana farin cikinsa kan haɓakar GOCOP da tasirinta, yana mai cewa burin iyayengidan da suka kafa ƙungiyar shi ne haɓaka aikin jarida na yanar gizo mai inganci da kuma tsaftace shi saboda kafofin sadarwa na yanar gizo suna tasowa kuma wasu mutane suna gunaguni game da yawaitar kafofin yanar gizon tare da sauran batutuwa. 


Ya ce, shi da sauran shugabannin farko na ƙungiyar, gami da marigayi tsohon shugaban GOCOP, Dotun Oladipo, suna son duk wanda ya shiga GOCOP ya fahimci nauyin gaskiya da ri}on amana.


Ya bayyana farin ciki cewa GOCOP ta yau tana ci gaba da riƙe falsafar aikin jarida mai inganci daga gare shi (Agbo) zuwa Mojeed Musikilu zuwa Dotun Oladipo zuwa Dr. Maureen Chigbo da yanzu Danlami Nmodu mni. Ya ba da wa]ansu shawarwari na dabarun gudanarwa kan yadda za a ]ore da ruhi da ci gaban ƙungiyar.

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 9 + 3?