Engr. Muttaqha-Rabe Darma , PhD
Akwai Abota Mai Karfi Wadda Kalmomi Ba Za Su Iya Bayyana Taba, Haka Kuma Akwai Kyawawa Abubuwan Tunawa Waɗanda Ba Za Su Taɓa Gushewa Ba. A Yau, Zuciyata Tana Cike Da Baƙin Ciki Sakamakon Rasuwar Babban Abokina, Aminin Oga, Sale Jari.
Abokin Oga, Tun Daga Rayuwar Su Ta Makarantar Firamare Har Zuwa Lokacin Da Mutuwa Ta Raba Su , Sun Kasance Da Kyakkyawar Abota Wadda Ta Wuce Yadda Ake Zato. Ƙalubale, Dariya Da Kuma Lokutta Masu Daraja Da Ba Za'a Taɓa Mantawa Da Su Ba.
Har Ma Suna Kwana A Kan Tabarma Ɗaya. SUN Taɓa Yin Tafiye-Tafiye A Kan Babur Daga Katsina Zuwa Kano Ko Kaduna, Kawai Don Kallon Tsofaffin Fitattun Fina-Finan Indiya Kamar Nagin Da Burning Train. Sun Kuma Yi Tafiya Zuwa Legas A Cikin Tsofaffin Motoci Marasa Ƙarfi, Suna Ƙirƙirar Abubuwan Tunawa Waɗanda Za Su Ci Gaba Da Kasancewa A Zuciyata Har Abada.
Sale, Rasuwarsa Ta Bar Babban Giɓi Mai Raɗaɗi A Cikin Zuciyar Engr. Darma, Abubuwan Da Suka Yi Tare Zasu Kasance A Matsayin Wani Ɓangare Na Rayuwata Har Abada. Ko Da Yake Mutuwa Ta Ɗauke Ka Daga Wannan Duniya, Ba Za Ta Taɓa Iya Goge Kyakkyawar Abotar Da Suka Yi Ba.
Kamar Yadda Muke Cewa, “KOWA YA MUTU, BAI SAURI BA; MU DA MUKE NAN BA MU DAƊE BA. SAI MUN ZO, Sale Jari.” Mutuwa Tafiyace Da Dukkanmu Zamuyi Wata Rana, Kuma Da Yardar Allah, Wata Rana Zamu Sake Haɗuwa A Aljanna Firdausee.
Ina Roƙon Allah Ya Gafarta Maka Kurakuranka, Ya Haskaka Kabarinka, Allah Ta'ala Ya Baka Jannatul Firdausee Alfarmar Sayyaduna Rasulillahi.


Comments (0)
No comments yet. Be the first to share your thoughts!