Gwamnatin Katsina Na Dab Da Kafa Wani Tarihi Da Kammala Hedkwatar Hukumar Sufuri

Daga wakilanmu.@ katsina TimesGwamnatin Jihar Katsina na dab da sake kafa wani tarihi a fannin sufuri, yayin da take shirin kammala aikin gina sabuwar hedkwatar Hukumar Sufuri ta Jihar Katsina…

Katsina City News September 23, 2026  ·  12:00 AM
| 80 Views
Gwamnatin Katsina Na Dab Da Kafa Wani Tarihi Da Kammala Hedkwatar Hukumar Sufuri
Gwamnatin Katsina Na Dab Da Kafa Wani Tarihi Da Kammala Hedkwatar Hukumar Sufuri


Daga wakilanmu.@ katsina Times


Gwamnatin Jihar Katsina na dab da sake kafa wani tarihi a fannin sufuri, yayin da take shirin kammala aikin gina sabuwar hedkwatar Hukumar Sufuri ta Jihar Katsina da ke Dandagoro, cikin birnin Katsina.

Binciken da muka gudanar ya nuna cewa, tashar sufuri ta kasance irin ta farko da wata hukumar sufuri ta jiha ta mallaka a Najeriya, musamman duba da irin tsari da kayan more rayuwar da aka tanada a cikinta.


An gina hedkwatar ne bisa tsarin zamani, tare da samar da kayayyakin more rayuwa da wuraren gudanar da ayyukan sufuri daban-daban. Binciken ya nuna cewa babu wata hukumar sufuri ta jiha a Najeriya da ke da hedkwata mai irin wannan tsari.

A cikin tashar akwai katafaren ginin ofishin gudanarwa, wanda ya kunshi ofisoshi masu yawa da aka tanada domin gudanar da ayyukan hukumar.


Haka kuma, an samar da babban wurin gyaran motoci idan sun samu matsala, tare da katafaren ɗakin ajiye kayayyakin gyaran motoci da spare parts, da kuma ofisoshin ma’aikata. Wurin gyaran motocin na da damar karɓar aƙalla motoci 30 a lokaci guda domin gyara.

Hedkwatar ta kuma ƙunshi katafaren masallaci mai sassan maza da mata, wanda ya isa gudanar da sallar Juma’a.

Advertisement

NRS Gateway

Bugu da ƙari, an samar da katafaren ɗakin cin abinci mai sassa daban-daban, ciki har da wurin da talakawa za su ci abinci, wurin musamman ga iyalai, da kuma wuraren hutawa da cin abinci.

Haka kuma, an tanadi ofishin ‘yan sanda a wani bangare na tashar domin taimakawa wajen tabbatar da tsaro da bin doka da oda.

A bangaren tashar motocin kuwa, an tsara rumfunan hutawa da saukar fasinjoji ta yadda motoci har guda 50 za su iya yin layi a lokaci guda, suna ɗaukar fasinjoji.


An kuma samar da kujeru a cikin rumfunan, inda fasinjoji za su iya zama cikin kwanciyar hankali yayin da suke jiran motar da za su hau ko kuma lokacin da suke jiran tafiya.

Daga cikin abubuwan da aka tanada akwai kuma gidan mai, wanda zai ba motocin da ke amfani da tashar damar sayen mai, tare da yi wa sauran masu ababen hawa da ke wucewa hidima.

Binciken ya nuna cewa irin wannan tsari da cikakken tanadin wuraren gudanar da harkokin sufuri ba kasafai ake samunsa a hedkwatar hukumar sufuri ta jiha a Najeriya ba, abin da ya sanya aikin ya zama wani babban shiri da zai iya zama abin koyi a fannin sufuri.

An fara aikin gina wannan katafaren shiri ne a zamanin tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Ibrahim Masari CFR, yayin da gwamnatin Gwamna Malam Dikko Umar Radda ke ci gaba da aikin domin ganin an kammala shi.


Idan aka kammala aikin tare da fara amfani da dukkan abubuwan da aka tanada, hedkwatar na da damar zama ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin sufuri na zamani da aka samar a matakin jiha a Najeriya.


Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 1 + 2?