Atiku zai maido da tallafin man fetur da Tinubu ya cire — amma kan sabon tsari

Daga Zaharaddeen Ishaq AbubakarTsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, ya ce zai dawo da wani sabon tsarin tallafin man…

Katsina City News August 20, 2026  ·  12:00 AM
| 94 Views
Atiku zai maido da tallafin man fetur da Tinubu ya cire — amma kan sabon tsari
Atiku zai maido da tallafin man fetur da Tinubu ya cire — amma kan sabon tsari

Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, ya ce zai dawo da wani sabon tsarin tallafin man fetur idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a 2027, domin rage wahalhalun da cire tallafin ya jefa ’yan Najeriya a ciki.

Atiku ya ce sabon tsarin ba zai kasance kamar tsohon tsarin tallafin da aka daina ba, inda za a mayar da hankali kan tallafa wa samar da man fetur a matatun cikin gida maimakon tallafa wa shigo da mai daga ƙasashen waje.

Ya bayyana shirin ne cikin Atiku Economic Recovery Plan (AERP) 2027, yana mai cewa tallafin zai kasance da iyaka, kasafin kuɗi da tsarin sa ido domin tabbatar da cewa amfanin tallafin ya isa ga jama'a.

A cewarsa, matatun mai na gwamnati da masu zaman kansu da suka cika sharudda za su samu ɗanyen mai na cikin gida a farashi mai sauki, amma za a tilasta musu tabbatar da cewa an tace man a Najeriya kuma an samar da kayayyakin man fetur da za su amfani kasuwar cikin gida.

Atiku ya ce za a bibiyi rabon ɗanyen mai, adadin da kowace matata ta karɓa, yawan man da ta tace da kuma wanda ta kai kasuwa, domin tabbatar da cewa ba a karkatar da tallafin zuwa amfanin wasu mutane ko kasuwannin ƙasashen waje ba.

Ya ce duk wata matatar da ta karkatar da ɗanyen mai ko kayayyakin man fetur da aka tallafa mata, ta karya ƙa’idojin samarwa ko ta kasa isar da amfanin tallafin ga ’yan Najeriya, za ta rasa cancantar ci gaba da cin gajiyar shirin tare da fuskantar matakin doka.

Atiku ya ce za a sanya wa sabon tsarin iyakar kuɗin da gwamnati za ta kashe a kowace shekara, kuma Majalisar Dokoki ta Ƙasa za ta amince da kudin ta hanyar kasafin kuɗi.

Ya ce yayin da samar da man fetur a cikin gida ke ƙaruwa, matatun mai ke samun inganci sannan farashin tace man ya ragu, za a rage tallafin a hankali har zuwa lokacin da ba za a sake buƙatarsa ba.

Ya ce manufar ba wai kawai rage farashin fetur ba ce, illa rage kuɗin sufuri, abinci da samar da kayayyaki, tare da ƙara ƙarfin saye ga ’yan Najeriya.

Advertisement

NRS Gateway

Atiku ya soki matakin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ɗauka na cire tallafin man fetur a ranar 29 ga Mayun 2023, yana cewa matakin ya jawo tashin farashin fetur, sufuri da kayan abinci.

Ya kuma yi tambaya kan wasu kuɗaɗen da NNPCL ta bayyana a bayanan kuɗaɗenta, yana cewa akwai buƙatar gwamnati ta yi cikakken bayani kan abin da kuɗaɗen suka ƙunsa da kuma ko suna da alaƙa da wasu nau’o’in tallafin man fetur.

Atiku ya ce NNPCL ta bayyana kashe kimanin ₦4.84 tiriliyan a matsayin Energy Security Expenses a shekarar 2023 da kuma ₦7.13 tiriliyan a shekarar 2024.

Ya ce idan gwamnati na ci gaba da ɗaukar bambancin farashin man fetur duk da cewa an sanar da kawo ƙarshen tallafi, to ya kamata a bayyana wa ’yan Najeriya yadda hakan ya bambanta da tsarin tallafin da aka ce an cire.

Atiku ya kuma yi kira da a yi cikakken bayani kan kimanin ₦30 tiriliyan da ya ce sun bayyana a cikin bayanan kuɗaɗen Asusun Tarayya, ciki har da kuɗaɗen shiga, cire-cire, tanadi da sauran mu'amaloli.

Sai dai ya jaddada cewa ba ya cewa wannan adadin kuɗin tallafin man fetur ne ko kuma an tabbatar da satar sa.

Ya ce abin da yake buƙata shi ne cikakken bayanin da zai nuna inda kuɗaɗen suka fito, yadda aka kashe su, waɗanda suka amfana da su da kuma tushen dokar da aka yi amfani da ita.

Atiku ya ce idan aka ba shi damar jagorantar ƙasar, za a sake binciken mu'amalolin da suka shafi tallafin man fetur na baya, kuma duk wanda aka tabbatar da cewa ya karkatar da kuɗaɗen gwamnati zai fuskanci hukunci bisa doka.

Ya ce sabon tsarin zai mayar da tallafin zuwa samar da man fetur a Najeriya, tare da sanya iyaka, bin diddigin kowace ganga da kuma duba sakamakon shirin, har sai an gina masana'antar tace man fetur da za ta iya tafiyar da kanta ba tare da tallafin gwamnati ba.

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 1 + 6?